Masar Ta Kafa Majalisar Kasa Ta Fada Da Ta'addanci A Kasar
Gwamnatin kasar Masar ta sanar da kafa wata majalisa ta kasa mai karfin iko don fada da ta'addanci da cikin shekarun nan yake ci gaba da barazana ga tsaro da zaman lafiyan kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a jiya Laraba ce gwamnatin kasar Masar din cikin wata doka da fadar shugaban kasar ta fitar inda ta ce dokar da ta kafa wannan majalisar ta ba da karfin tsara hanyoyi da siyasar da za a bi wajen fada da ta'addanci da tsaurin ra'ayi.
Majalisar dai za ta kasance ne karkashin jagorancin shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi kuma za ta kumshi shugaban majalisar kasar, firayi minista, shugaban jami'ar al-Azhar ta kasar bugu da kari kan wasu ministoci.
A halin yanzu dai kasar Masar din tana cikin fada da kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban a kasar musamman a lardin Sinai wadanda suka kashe daruruwan sojoji da 'yan sandan kasar tun daga shekarar 2013.