Karya yarjejjeniyar tsakaita wuta a kasar Sudan ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2263-karya_yarjejjeniyar_tsakaita_wuta_a_kasar_sudan_ta_kudu
Duk da cewa an fara aiki da yarjejjeniyar sulhu a kasar Sudan ta kudu, amma har yanzu ana fuskantar matsalar karya yarjejjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangaren 'yan tawaye da Gwmnati
(last modified 2018-08-22T06:57:58+00:00 )
Mar 11, 2016 05:06 UTC
  • Karya yarjejjeniyar tsakaita wuta a kasar Sudan ta Kudu

Duk da cewa an fara aiki da yarjejjeniyar sulhu a kasar Sudan ta kudu, amma har yanzu ana fuskantar matsalar karya yarjejjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangaren 'yan tawaye da Gwmnati

Kafar watsa labaran Afirka time ta habarta cewa An kai hari a yankin Assir dake jihar Nil Aliya,inda dukkanin bangarorin biyu ke zarkin junansu da kai harin,a cewar Marko Mayol Kakakin Gwamnatin rikon kwaryar kasar, bangaren 'yan tawaye ne ya kai harin baya bayan nan a guraren Sojojin dake biyayya da Gwamnati,inda suka fuskanci martani daga Sojojin kasar.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da ake karya yarjejjeniyar tsakaita wuta a kasar Sudan ta Kudun, inda a ko wani lokaci bangarorin biyu ke zarkin juna da karya da yarjejjeniyar.

A shekarar 2011 ne Sudan ta kudu ta samu 'yan cin kanta daga kasar Sudan, bayan shekaru biyu kacal,kasar ta fuskanci rikicin siyasa bayan da Shugaba Salva Kiir ya kori mataimakinsa Riek Mashar daga kan mikaminsa,inda shi kuma ya dauki makamai, lamarin da ya yi sanadiyar lashe rayukan mutane da dama.A watan Augustan shekarar da ta gabata, bangarorin biyu sun cimma yarjejjeniyar sulhu, lamarin da ya kawo karshen zubar da jini a kasar