Sarkin Marocco Ya Yi Wa Fursunoni Da Dama Ahuwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22720-sarkin_marocco_ya_yi_wa_fursunoni_da_dama_ahuwa
Sarki Mohammed na shida na Marocco ya yi wa fursunoni da dama ahuwa ciki har da wadanda aka cafke a yayin zanga zanga yankin rif dake arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:28+00:00 )
Jul 30, 2017 01:50 UTC
  • Sarkin Marocco Ya Yi Wa Fursunoni Da Dama Ahuwa

Sarki Mohammed na shida na Marocco ya yi wa fursunoni da dama ahuwa ciki har da wadanda aka cafke a yayin zanga zanga yankin rif dake arewacin kasar.

Jim kadan gabanin jawabin shekarunsa 18 da hawa sarautar kasar, wata sanarwa daga ma'aikatar shari'ar kasar ta ce sarki Mohammed na shida ya yi ahuwa ga fursuna 1,178 cikinsu kuwa har da mambobin gungun masu bore na birnin Al-Hosaima da kewaye.

Duk da cewa sanarwar bata bayyana adadin 'yan boren da ahuwar ta shafa ba, aman ta ce mafi yawasu wadanda basu yi kisan kai  ko kuma babban laifi ba.

Saidai wata majiya daga gwamnatin kasar ta shaida cewa mutane 40 ne akayi wa ahuwa daga cikin masu boren, amman banda jagoran masu boren.

Lauyen dake kare masu boren ya danganta batun da ci gaba, aman ya kamata a saki duk wadanda ake tsare da.