Najeriya : Mahajjatan Farko Sun Isa Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22764-najeriya_mahajjatan_farko_sun_isa_saudiyya
Tawagar ta farko na mahajjatan bana daga jihar Sokoto a tarayyar Nijeriya sun isa kasar mai tsari a yau Litinin.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jul 31, 2017 11:22 UTC
  • Najeriya : Mahajjatan Farko Sun Isa Saudiyya

Tawagar ta farko na mahajjatan bana daga jihar Sokoto a tarayyar Nijeriya sun isa kasar mai tsari a yau Litinin.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto Ibrahim Umar shugaban hukumar mahajjata na jihar yana fadar haka a yau litinin, ya kuma godewa gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal kan taimakon da ya bayar don ganin an mahajjan jihar sun gudanar da ayyukan hajji kamar yadda ya dace. 

Shugaban hukumar ya kara da cewa sun gargadi mahajjata da su gujewa daukar muggan kwayoyi tare da su zuwa kasar saudia, don duk wanda aka kama za'a mika shi ne ga hukumomin da suka dace.

A Jihar kwara kuma hukumar mahajjatan jihar ce ta fidda sunayen maniyyata mata ukku sanadiyyar samunsu da danyen ciki.

A Abuja kuma babban birnin kasar an fara jigilar mahajjatan ne tun jiya Lahadi, inda kamfanin jiragen sama na FlyNas Airline, Azman Airline da kuma Max Air suka fara aikin jigilar.

Manajan Tashar jirgaen sama na Namdi Azikuwe Engr Sale Dunoma ya tabbatarwa dailtrust kan cewa ma'aikatansa a shirye suke don gudanar da aikin jigilar mahajjata na wanna  shekara. Ya kuma bukaci maniyyata daga birnin su fito zuwa sansanin mahajjata a lokutan da aka tsara masu don kada wani rasa jirgin da zai kaisu kasar saudia.