Kotun Kasar Malawi Ta Bayar Da Umarnin Kame Tsohuwar Shugabar Kasar
(last modified Tue, 01 Aug 2017 07:31:06 GMT )
Aug 01, 2017 07:31 UTC
  • Kotun Kasar Malawi Ta Bayar Da Umarnin Kame Tsohuwar Shugabar Kasar

Kotun kasar Malawi ta bayar da umarnin kame tsohuwar shugabar kasar Joyce Hilda Banda, bisa zarginta da halasta kudaden haram.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar 'yan sandan kasar Malawi ya fadi a jiya cewa, kotu ta ba su umarnin kamo tsohuwar shugabar kasar domin gurfanar da ita a kan zarginta da hannu a wawure wasu kudaden gwamnati.

Tun bayan da Joyce Hilda Banda ta sha ka yi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Malawi a cikin shekara ta 2014, ta koma Amurka da zama, amma a cikin wata sanarwa da ta fitar a kwanakin baya, ta bayyana cewa za ta koma kasarta ba da jimawa ba.