Kotun Masar Ta Wanke Dan 'Uwan Shugaban AlQa'ida.
(last modified Tue, 01 Aug 2017 13:01:00 GMT )
Aug 01, 2017 13:01 UTC
  • Kotun Masar Ta Wanke Dan 'Uwan Shugaban AlQa'ida.

Wata Kotu a Masar ta wanke dan'uwan shugaban kungiyar ta'addancin nan ta alka'ida kan zarkin da ake yi masa na kafa kungiyar masu tsatsauran ra'ayin addini.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto majiyar shara'ar kasar masar na cewa, a karshen shara'ar da aka gudanar jiya litinin kotu ta wanke Muhamad Zawahiri, dan'uwan shugaban kungiyar alka'ida kan zarkin da ake yi masa na kafa kungiyar masu tsatsauran ra'ayin addini, da suke kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati.

Kafin hakan  dai, a shekarar 2015 kotun hukunta manyan laifuka ta birnin alkahira ya wanke zawahiri tare da wasu mutane 16 da ake zarki da kai hare-haren kan gine-ginen gwamnatin kasar.

Tun bayan da aka sauke Muhamad Mursi tsohon Shugaban kasar ta Masar, aka kama Muhamad Zawahiri tare da wasu mutane 57, kan zarkin kafa kungiya ba kan ka'ida ba, tare kuma da daukan makami,gami da kai hare-haren a wajen kasar ta Masar.