An Kashe Wani Babban Jami'in Hukumar Zaben Kasar Kenya.
A yayin da ya rage kasa da maku guda a gudanar da zaben shugaban kasa a kenya, wasu 'yan bindiga sun hallaka wani babban jami'in hukumar zaben kasar
Hukumar 'yan sandar kasar Kenya ta sanar da cewa a ranar juma'ar da ta gabata wasu 'yan bindiga sun yi awan gaba da Grace Amtsando da ya kasance daga cikin jami'an masu sanya ido a zaben Shugaban kasar da zai gudanar cikin maku mai kamawa, inda suka hallaka shi sannan kuma suka yada gawarsa a kusa da makabartar Nairobi babban birnin kasar.
Har ila yau a ranar Assabar din da ta gabata, wani dan bindiga ya kai hari gidan William Reto mataimakin shugaban kasar Kenya, inda ya kashe jami'in tsaron dake kula da lafiyarsa.
Irin wannan kisa da aka yiwa manyan jami'an gwamnati a kasar na iya tasiri a harakokin zaben kasar.
A bangare guda, kungiyar Ashabab ta kasar Somaliya ta sanar da cewa za tayi iya kokarinta domin wargaza matakan tsaron da aka dauka yayin gudanar da zabe a kasashen Kenya da Uganda.
A ranar 8 ga watan Augustan da muke ciki ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a kenya, inda Shugaba mai barin gado Uhuru kinyata zai fafata da abokin hamayyarsa Raila Odinga madugun 'yan adawar kasar.