Kungiyar Ashabab Ta Kwace Wani Gari A kudancin Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22884-kungiyar_ashabab_ta_kwace_wani_gari_a_kudancin_somaliya
Mayakan Ashabaab sun kwace garin Leego da ke a kudancin kasar Somaliya, jim kadan bayan barin garin da sojojin tabbatar da zaman lafiya suka yi.
(last modified 2018-08-22T07:00:29+00:00 )
Aug 04, 2017 14:31 UTC
  • Kungiyar Ashabab Ta Kwace Wani Gari A kudancin Somaliya

Mayakan Ashabaab sun kwace garin Leego da ke a kudancin kasar Somaliya, jim kadan bayan barin garin da sojojin tabbatar da zaman lafiya suka yi.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto wata majiya ta kasar Somaliya na cewa a wannan juma'a mayakan kungiyar ta'addancin ta Ashabaab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida sun mamaye  garin Leego da ke a kudancin kasar Somaliya, jim kadan bayan barin garin da sojojin tabbatar da zaman lafiya suka yi.

Garin mai nisan kilomita 80 dake yankin arewa maso yammacin Mogadishu babban birnin Somaliyar, yanki ne da 'yan bindigar suka kashe akalla mutane 12 a makon da ya gabata.

Wani mazaunin garin Farah Ahmed, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar da sanyin safiyar yau juma'a ne dai dakarun tsaron na zaman lafiya suka bar garin da lamarin ya faru.

Yanzu dai yankin na hannun Sheikh Abdi asis Abu Musab da ke a matsayin  jigo a kungiyar ta Ashabab.