Najeriya: An Kashe 'Yan Ta'adda 3 A Jahar Borno
Aug 05, 2017 14:18 UTC
Jami'an tsaron kasar sun sanar da cewa dukkanin 'yan ta'addar uku da aka kashe suna kokarin kai harin kunar bakin wake ne.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin da ya nakalto labarin ya kara da cewa;Lamarin ya faru ne a yankin Usmanti a jahar ta Borno.
Jami'an tsaro sun rika bin diddigin maharan ne har zuwa wani wuri da su ka killace su,inda su kuma nan take suka tarwatsa bama-baman da su ka yi jigida da su. Biyu daga cikin jami'an tsaro sun jikkata.
Jahar ta Borno dai tana fama da matsalar tsaro saboda hare-haren da 'yan ta'addar kungiyar Boko haram su ke kai wa. Tare da cewa a baya an sami sauki hare-haren na ta'addanci, sai dai a cikin watanni biyu na bayan nan sun tsananta.
Tags