Ethiopia Za Ta Taimaka Wa Somali Kwato Garin Leego Daga Al-Shabaab
Gwamnatin kasar Ethiopia ta sanar da cewa za ta tura sojojinta zuwa kasar Somaliya da nufin taimakawa wajen sake kwato garin Leego mai tsananin muhimmanci da 'yan kungiyar Al-Shabaab suka kwace a ranar Juma'a.
Rahotanni daga kasar sun bayyana cewar tawagar sojojin kasar Ethiopian da suka isa garin Baidoa su ne za su shiga cikin shirin da ake yi na kwato garin Leego din daga hannun 'yan kungiyar ta'addancin na Al-Shabaab.
Garin Leego din dai wani gari ne mai matukar muhimmanci da ya hada birnin Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya da kuma garin Baidoa, dakarun Al-Shabab din sun kwace garin ne bayan da dakarun kungiyar Tarayyar Afirka da kuma na kasar Somaliyan sun bar wajen, har ya zuwa yanzu dai ba a tantance dalilin barinsu garin.
Ethiopia dai tana daga cikin kasashen da suke fada da 'yan kungiyar Al-Shabab din na kasar Somaliya saboda barazanar da suke yi wa tsaron kasar Ethiopian.