An Yi Awan Gaba Da Fasinjoji Da Dama A Kudancin Najeirya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22990-an_yi_awan_gaba_da_fasinjoji_da_dama_a_kudancin_najeirya.
Wasu 'yan bindiga sun yi awan gaba da fasinjsar Bas 16 jiya Litinin a Kudancin Najeriya.
(last modified 2018-08-22T07:00:30+00:00 )
Aug 08, 2017 02:18 UTC
  • An Yi Awan Gaba Da Fasinjoji Da Dama A Kudancin Najeirya.

Wasu 'yan bindiga sun yi awan gaba da fasinjsar Bas 16 jiya Litinin a Kudancin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto wata majiyar tsaron kudancin Najeriya na cewa, a jiya Litinin wasu 'yan bindiga sun tare wata babbar hanya tare da buda wuta a kan wata motar fasinja ta Bas a kusa da garin fatakol  mai arzikin man fetur dake kudancin kasar, inda suka yi awan gaba da fasinjoji 16 daga cikin su har da matukin matar.

Shaidu da ido sun bayyana cewa 'yan bindigar sun fice da mutanan zuwa yankunan jeji, a nasu bangare jami'an 'yan sandar jihar Rives sun tabbatar da aukuwar lamarin, tare da bayyana cewa tuni suka fara gudanar da bincike domin zagulo wadanda suka aikata wannan laifi.

Ya zuwa yanzu babu wani gungu da ya dauki alhakin sace mutanan, to saidai satar mutane tare da neman kudin fansa ba wani sabon abu ba ne a kudancin Najeriya, inda wasu matasan suka mayar da shi sana'a a kudasncin kasar.