Najeriya: An Sace Motar Safa Mai Dauke Da Mutane 16
Aug 08, 2017 07:41 UTC
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto cewa; Masu dauke da makamai sun tsare motar ne a kusa da birnin Port Harcout inda su ka yi garkuwa da mutanen cikinta 16
Majiyar 'yan sanda a garin na Por Harcourt sun tabbatar da faruwar lamarin, sannan kuma su ka sanar da cewa sun fara binciken ganon maharan.
Kawo ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan ko su waye maharan.
Satar mutane domin karbar fansa ta zama ruwan dare a cikin wasu yankuna na Najeriya.
Watannin baya ne dai jami'an tsaron kasar su ka kama Evans wanda ya shahara da satar mutane domin karbar fansa.
Tags