Sharhi: Zaben Kasar Kenya Da Muhimmancin Zaman Lafiya Ga Ci Gaban Kasar
(last modified Wed, 09 Aug 2017 05:51:38 GMT )
Aug 09, 2017 05:51 UTC
  • Sharhi: Zaben Kasar Kenya Da Muhimmancin Zaman Lafiya Ga Ci Gaban Kasar

Rahotanni daga kasar Kenya suna nuni da cewa ana ci gaba da kidayen kuri'un da aka kada a zabubbukan da aka gudanar a jiya Talata a kasar, inda shugaba mai ci Uhuru Kenyatta yake kan gaba a zaben shugaban kasar, duk kuwa da korafe-korafen da 'yan adawa suka fara yi.

A bangaren zaben shugaban kasa, wanda shi ne ya fi daukar hankula, 'yan takara takwas ne dai suke fafatawa a tsakaninsu, duk kuwa da cewa asalin gasar dai tsakanin 'yan takara biyu ne wato shugaba mai ci Uhuru Kenyatta wanda yake neman wa'adi na biyu kuma na karshe na shugabancin kasar da kuma madugun 'yan adawa Raila Odinga, wanda wannan shi ne karo na hudu da ya tsaya takarar shugabancin kasar Kenyan.

An gudanar da zaben kasar Kenyan ne dai cikin yanayi na dar-dar na yiyuwar barkewar rikici musamman bayan sanar da sakamakon zaben. Rikici mafi muni cikin zabubbukan kasar Kenyan ya faru ne bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2007 lokacin da 'yan adawan karkashin jagorancin Mr. Odinga suka yi ikirarin an yi magudi, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 1000 kana wasu dubban kuma suka sami raunuka, lamarin da ya kusan sanya kasar cikin yakin basasa.

Hukumar zaben kasar dai ta sanar da cewa sama da mutane miliyan 20 ne suka cancanci kada kuri'arsu a zaben, a saboda haka ne ma kungiyoyi da jam'iyyun siyasa suka ta kiran magoya bayansu da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri'arsu saboda muhimmancin da zaben na bana yake da shi, duk kuwa da cewa asalin gasar dai tsakanin 'yan takara biyun da muka ambata a baya ne.

Duk da cewa rahotanni sun nuna cewa tsawon makonnin da suka gabata babu wani abin damuwa sosai dangane da faruwar rikici a kasar Kenyan, to amma kisan gillan da aka yi wa Christopher Msando, daya daga cikin manyan jami'an hukumar zaben kasar, ya janyo kace-nace da kuma sanya tsoro cikin zukatan wasu na yiyuwar faruwar magudin zabe wanda hakan zai iya sanya kasar cikin yanayi na rikici.

Kasar Kenya dai wacce daya ce daga cikin manyan kasashen Afirka tana da girman matsayi a siyasar nahiyar Afirkan. To sai dai duk da haka tana fuskantar matsaloli da dama, daya daga cikinsu kuwa shi ne matsalar tsaro sakamakon ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda musamman 'yan kungiyar nan ta Al-Shabab na kasar Somaliya. A bangare guda kuma ga matsalar 'yan gudun hijirar da suke shigowa kasar daga kasashen makwabta, haka nan kuma ga matsalar rashawa da cin hanci. Dukkanin wadannan matsaloli ne da suka yi tasiri cikin ra'ayin al'ummar kasar da kuma zaban dan takaran da suke ganin zai iya magance musu su.

Koma dai mene ne abin da dai yake a fili shi ne gudanar da ingantaccen zabe da kuma amincewa da sakamakonsa, ko waye kuwa ya ci zaben, lamari ne da zai iya kare kasar daga fadawa cikin rikici irin na shekara ta 2007.