Kenya: An Kashe Wasu Masu Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Sakamon Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23038-kenya_an_kashe_wasu_masu_zanga_zangar_kin_amincewa_da_sakamon_zabe
Rahotanni daga kasar Kenya na cewa, akalla mutane biyu ne daga cikin masu zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa aka tabbatar da mutuwarsu, sakamakon wata taho mu gama da jami'an tsaro.
(last modified 2018-08-22T07:00:31+00:00 )
Aug 09, 2017 12:09 UTC
  • Kenya: An Kashe Wasu Masu Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Sakamon Zabe

Rahotanni daga kasar Kenya na cewa, akalla mutane biyu ne daga cikin masu zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa aka tabbatar da mutuwarsu, sakamakon wata taho mu gama da jami'an tsaro.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar biyu sun mutu ne sakamakon harbi da bindiga da 'yan sanda suka yi a kan masu zanga-zangar a yau Laraba a garin Safi.

Wani jami'in 'yan sanda ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa barayi ne suka shiga cikin masu zanga-zangar domin wawushe kayan jama'a, a kan haka suka yi amfani da karfi domin tarwatsa su.

Madugun adawa na kasar Kenya Reila Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a  jiya a kasar, inda ya zargi Uruhu Kenyatta da hukumar zaben kasar da tafka magudi.