Hamma Amadou Zai Shiga Zagaye Na Biyu Na Zaben Niger
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2305-hamma_amadou_zai_shiga_zagaye_na_biyu_na_zaben_niger
Lauyan jagoran 'yan adawa a Nijar Hama Amadou, Mossi Boubacar ya sanar da cewa Hama Amadou zai shiga zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 20 ga watan Maris din nan sabanin sanarwar da aka yi a baya na cewa ba zai tsaya din ba.
(last modified 2018-08-22T06:57:58+00:00 )
Mar 12, 2016 05:29 UTC
  • Hamma Amadou Zai Shiga Zagaye Na Biyu Na Zaben Niger

Lauyan jagoran 'yan adawa a Nijar Hama Amadou, Mossi Boubacar ya sanar da cewa Hama Amadou zai shiga zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 20 ga watan Maris din nan sabanin sanarwar da aka yi a baya na cewa ba zai tsaya din ba.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo Lauya Mossi Boubacar yana fadin cewa, Hama dai bai janye daga zaben. Har yanzu shi dan takara ne na gammayar jam'iyyun 'yan adawa na kasar wato COPA, duk kuwa da cewa gamayyar jam'iyyun adawar ta COPA sun ce ba za su shiga zaben ba, amma Hama zai shiga.

Sanarwar lauyar dai ta sake sanya rudu cikin makomar zaben don kuwa a baya gamayyar jam'iyyun adawar ta ce dan takararta Hama Amadou ba zai shiga zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ba, kamar yadda kuma kakakin jam'iyyar Moden Lumana ta Hama Amadou, Mahaman Laouali Leger ya sanar da cewa Haman Amadoun ya amince da matakin da COPA ta dauka.

Hama Amadou, wanda kuma shi ne tsohon shugaban majalisar kasar ta Nijar yana tsare a gidan yari sakamakon zargin da ake masa na fataucin jarirai.

Hukumar zaben kasar CENI dai ta sanar da cewa tana kan bakarta na ci gaba da gudanar da zagaye na biyu na zaben koda kuwa 'yan adawar basu shiga zaben ba.