Kenya Bayan Zabe: A kalla Mutane Uku Ne Su Ka Mutu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23058-kenya_bayan_zabe_a_kalla_mutane_uku_ne_su_ka_mutu
Jami'an tsaron kasar a yankin Tana River sun sanar da kashe mutane 3 bayan da su ka kai hari da wukake a wata cibiyar zabe.
(last modified 2018-08-22T07:00:31+00:00 )
Aug 10, 2017 07:53 UTC
  • Kenya Bayan Zabe: A kalla Mutane Uku Ne Su Ka Mutu

Jami'an tsaron kasar a yankin Tana River sun sanar da kashe mutane 3 bayan da su ka kai hari da wukake a wata cibiyar zabe.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ce; Wasu mutane biyar ne su ka kai hari akaد cibiyar zabe ta Holaو da ke gundumar Tana River inda su ka jikkata mutum guda, sai dai jami'an tsaro sun kashe uku daga cikinsu.

Wata sanarwar ta jami'an tsaron kasar ta ce a cikin birnin Nairobi ma mutane uku sun mutu sanadiyyar taho mu gama a tsakanin bangarori biyu na masu goyon bayar shugaban kasa da 'yan adawa.

Bayan da jagoran 'yan hamayya Raila Odinga ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben shuagan kasa, magoya bayansa sun bazama kan tituna.