Somaliya: An Kashe Wani Babban Kwamandan al-Shabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23096-somaliya_an_kashe_wani_babban_kwamandan_al_shabab
Majiyar gwamnatin kasar ta Somaliya ta sanar da cewa; Wanda aka kashe din yana da hannu a hare-hare na ta'addanci a cikin babban birnin kasar Magadishu.
(last modified 2018-08-22T07:00:31+00:00 )
Aug 11, 2017 06:43 UTC
  • Somaliya: An Kashe Wani Babban Kwamandan al-Shabab

Majiyar gwamnatin kasar ta Somaliya ta sanar da cewa; Wanda aka kashe din yana da hannu a hare-hare na ta'addanci a cikin babban birnin kasar Magadishu.

Bayanin da  ma'aikatar sadarwa ta kasar Somaliyan ta fitar a jiya alhamis ya kunshi cewa; A cikin makwanni biyu da su ka gabata, jami'an tsaron kasar sun yi nasarar rusa  daya daga cikin gungun 'yan ta'addar da kuma kashe kwamandansu da ake kira da al-jibal.

 Shugaban kasar ta Somaliya Muhammad Abdullahi Muhammad, ya bai wa sojojin kasar umarni da su yi aiki tare da sojojin kasa da kasa wajen kai hari a yankin " Banadir" da ke birnin Magadishu.

Kungiyar ta al-shabab mai alaka da al-ka'ida tana ci gaba da zama barazana ga kasar ta Somaliya da kuma kasashen makwabta.