Gambiya : An Fara Binciken Yadda Jammeh Ya Tafiyar Da Harkokin Kudaden Baitulmali
Hukumar binciken da gwamnatin kasar Gambiya ta kafa domin duba yadda tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya tafiyar da harkokin kudaden baitulmalin kasar ta fara sauraron ra'ayoyin jama'a karo na farko.
An dai samu zarge-zarge masu karfi game da yadda aka tafiyar da harkokin kudaden kasar, kamar yadda wasu manajojin hukumomin kudaden kasar hudu suka ba da shaida a jiya Alhamis data gabata.
Shugaban hukumar binciken Surahatta Semega Janneh ya ce, babban dalilin da ya sanya aka gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'ar shi ne, domin tabbatar da cewa, an gudanar da aikin a bayyane karara.
Kamar yadda Surahatta Semega Janneh ya sanar, an kafa hukumar ne domin bincikar yadda tsohon shugaban kasar da mataimakansa suka tafiyar da sha'anin kudaden da dukiyoyinsa a lokacin da yake jan ragamar shugabancin kasar.
A kwanan baya ne dai Shugaban Gambiya, Adama Barrow ya kafa kwamitin da zai binciki dukiyar da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya mallaka, kuma an dorawa kwamitin nauyin bincikar yadda Jammeh ya tafiyar da wasu ma'aikatu da dukiyar da ya mallaka da kuma harkokin tafiyar da kudadensa da kuma na wasu mukarabansa.
A watan Mayu da ya gabata ne ministan shari'a na kasar, Abubakar Tambadu, ya sanar da toshe dukiyar da Mista Jammeh ya mallaka, bayan zargin da hukumomin kasar sukayi masa na karkata wasu kudade da yawansu ya kai Dala Miliyan hamsin.