Kenya: An Ci Gaba Da Samun Tashin Hankali Bayan Zabe.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23112-kenya_an_ci_gaba_da_samun_tashin_hankali_bayan_zabe.
Jim kadan bayan sanar da sakamakon zabe na karshe wanda ya bai wa shugaba Uhuru Kenyatta nasara, magoya bayan Raila Odinga sun bazama kan tiitunan birnin Nairobi.
(last modified 2018-08-22T07:00:31+00:00 )
Aug 12, 2017 04:47 UTC
  • Kenya: An Ci Gaba Da Samun Tashin Hankali Bayan Zabe.

Jim kadan bayan sanar da sakamakon zabe na karshe wanda ya bai wa shugaba Uhuru Kenyatta nasara, magoya bayan Raila Odinga sun bazama kan tiitunan birnin Nairobi.

Kamfanin dillancin labarun Spotnik ya ambato cewa; Magoya bayan Odinga din sun rika kai hare-hare a gidajen 'yan kabilar shugaban kasar tare da kobe su.

A can birnin Kisumu da ke yammacin kasar, wanda kuma  can ne cibiyar 'yan adawa, an rika jin hareb-harbe da bindigogi.

An girke  'yan sanda da su ka kai 180,000 a cikin yankunan kasar musmaman ma dia babban birnin kasar Nairobi.

Uhuru Kenyatta ya lashe zaben da kaso 54.27.

Tun ana kan kidaya sakamakon zaben ne dai dan takara Raila Odinga ya sanar da rashin amincewarsa, tare da yin zargin tafka magudi.