Kenya: Kungiyar Tarayyar Turai Ta Taya Kenyatta Murnar Lashe Zabe
Kungiyar tarayyar turai ta taya zababben shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta murnar sake lashe shugaban kasar da aka gudanar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, babbar jami'a mai kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta isar da sakon taya murna ga Kenyatta, kuma ta yi kira ga sauran bangarorin siyasar kasar da su kwantar da hankali, kuma a bi hanyoyi na sulhu domin warware matsalolin siyasar kasar.
Bayan sake zabensa a wa'adin mulki na biyu da kashi 54.27% na dukkanin kuri'un da aka kada, Uhuru Kenyatta ya kirayi abokin hamayyarsa Reila Odinga wanda ya samu kashi 44.74 da ya zo su hada kai domin yin aiki tare.
Sai a nasu bangaren gungun 'yan adawa sun ce ba za su taba mika wuya ba, kamar yadda wani na hannun damar Reila Odinga Johnson Motama ya fada a jiya.