Ambaliyyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutum 312 A Saliyo
Bayanai daga Saliyo na cewa a kalla mutane 312 ne suka rasa rayukansu a ibtila'in ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da laka data biyo bayan ruwan sama tamakar da bakin kwarya da aka samu a Freetown babban birnin kasar.
Ibtila'in ya kuma raba sama da mutane dubu biyu da muhallansu, a yayin da kuma ake da fargabar alkalumen mutanen da suka rasa rayukansu ya karu.
Wani wakiln kamfanin dilancin labaren AFP ya ce ya gane ma idanunsa gawarwakin mutane da dama da ruwa ya yi awan gaba da su da kuma gidaje masu yawa da laka ta rufe a kauyen Regent dake wajen birnin.
Wannan dai ita ce ambaliyar ruwa mafi muni da aka taba gani a nahiyar a cikin shekaru 20 da suka gabata.
Tuni dai gwamnatin kasar Saliyo ta yi wani taron gaggawa domin duba matakan dauka na tunkarar wannan iftila'in, a yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da kokarin zakulo wadanda lamarin ya rusa dasu.