Ana Zaman Makoki Bayan Harin Ta'addanci A Burkina Faso
A Burkina Faso an shiga zaman makoki na kwanaki uku tun daga jiya Litini bayan kazamin harin ta'addanci da ya yi sanadin mutuwar mutane 18 a wani gidan sayar da abinci a Ouagadugu babban birnin kasar.
A halin da ake ciki dai an tantance gawawakin mutane 15 daga cikin wadanda suka mutun, da suka hada da 'yan kasar ta Burkina Faso takwas da kuma 'yan asalin kasashen waje bakwai ( Bafaranshe guda, 'yar Canada guda, dan Senegal guda, dan Najeriya guda da dan Turkiyya da kuma 'yan Kuwait biyu).
A cikin daren ranar Lahadi data gabata ce wasu 'yan bindiga bisa mashin suka kai hari a gidan cin abunci na Turkawa dake Ouagadugu
Shugaban kasar ta Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré ya yi Allah wadai da harin.
A watan da ya gabata ne dai kasar Faransa da kasashen Afrika na gungun G5 Sahel da suka hada da Burkina Faso, Chad, Mali, Mauritania da Nijar, suka cimma matsaya ta kaddamar da runduna ta musamman mai yaki da 'yan tada kayar baya masu tsattsauran ra'ayi a yankin na Sahel.