Harin Ta'addanci A Kasar Burkina Faso. ( sharhi)
(last modified Wed, 16 Aug 2017 05:37:09 GMT )
Aug 16, 2017 05:37 UTC
  • Harin Ta'addanci A Kasar Burkina Faso. ( sharhi)

Harin Ta'addanci A Kasar Burkina Faso. ( sharhi)

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta sanar da mutuwar mutane 17 da kuma jikkatar wasu 8 sanadiyyar harin ta'addanci da aka kai wa wani Hotel a birnin  Ouagadougou .

Wanann harin ya yi kama da kwatankwacinsa da aka kai a Hotel din Splendid a cikin watan Janairu na 2016, da kuma wani harin da aka kai wa gidan cin abinci wanda ya ci rayukan mutane 40.

Tare da cewa shekaru masu tsawo kasar ta Burnika Faso, tana cikin kasashen yankin yammacin Afirka masu tsaro da zaman lafiya, amma a cikin shekarun bayan nan al'amurra sun sauya saboda kutsen kunkiyoyin ta'addanci. Iyakokin da kasar ta ke da ita da Kasashen Mali da Nijar, da kuma shigarta cikin kasashen da suke fada da kungiyoyin ta'addanci, suna daga cikin dalilan da su ka ja hankalin 'yan ta'adda kan wannan kasar.

Bullar Bokoharam a yankin yammacin Afirka musamman a kasar Najeriya, ya raba yankin da zaman lafiya da tsaro. Kuma duk da cewa ana jan daga da fada da wannan kungiyar ta 'yan ta'adda, amma duk da haka wuraren da take kai wa hari sun karu. Baya ga Najeriya kasar tana kai hari a cikin kasar Nijar.

A daya gefen, ci gaban rikice-rikice a kasar Mali ya sake bai wa 'yan ta'addar wata damar ta fadada hare-harensu a cikin yankin. Kuma a kodayaushe da akwai hatsarin kara yaduwar ayyukan ta'addanci a cikin yankin.

Ba da jimawa ba wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka, Muhammad Bin Chambas ya yi gargadi akan hare-hare masu hatsari akan iyakar kasar Mali. Haka nan hatsarin ayyukan ta'addanci a cikin kasashen Burkina Faso da kuma Nijar. 

Kasashen yankin na yammacin Afirka sun dade da fito da tsare-tsare na fada da ta'addanci da suka kunshi aiki tare domin kare kan iyakokinsu.

 

Daga cikin yunkuri na bayan nan da kasashen yankin Sahel suka yi shi ne kafa runduna ta kasashe biyar. Kasashen sune Nijar, Mali Burkina Faso, Chad da Murtaniya.

Wani masanin harkokin siyasa da zamantakewa na yankin, Amadu Alpha Ly yana fadin cewa:  "Rundunar kasashen biyar za ta rage yawan kai kawon da 'yan ta'addar suke yi, haka nan kuma ta'addancin da suke kai wa. Za ta kuma taka gagarumar rawa wajen fada da ta'addanci a wannan yankin na Afirka." 

 

Aiki tare da kasashen yankin suke yi a fagen fada da ta'addanci, ya sa wasu kungiyoyin ta'addancin suna fuskantar cikas fiye da baya. Wannan ne ya sa kungiyoyin suke son nuna kansu ta hanyar tsananta kai hare-hare a wasu kasashen.

 

Harin da aka kai a  Ouagadougou yana a matsayin maida martani ne mai karfi daga 'yan ta'addar saboda shiga da kasar Burkina Faso ta yi a cikin fada da kungiyoyin ta'addanci a yammacin Afirka. Manufarsa shi ne samar da tsoro da razana a cikin kasashen yankin. Sai dai duk da haka, kasashen yankin suna da kyakkyawan fatan samun nasara akan kungiyoyin 'yan ta'adda na yankin.