An Fara Zaman Makoki Na Mako Guda A Kasar Saliyo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23240-an_fara_zaman_makoki_na_mako_guda_a_kasar_saliyo
Gwamnatin kasar Saliyo ta sanar da zaman makoki na maku guda domin jimamin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwa.
(last modified 2018-08-22T07:00:33+00:00 )
Aug 16, 2017 14:47 UTC
  • An Fara Zaman Makoki Na Mako Guda A Kasar Saliyo

Gwamnatin kasar Saliyo ta sanar da zaman makoki na maku guda domin jimamin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwa.

Al'ummar kasar Saliyo sun fara zaman makoki na kwanaki bakwai a yau laraba domin jimami da nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da  suka yi sanadiyar mutuwar daruruwan jama'a.

Da yammacin wannan larba ce a gudanar da taron addu'oi na mabiya addinai daban daban a babban filin wasa dake Freetown babban birnin kasar inda iftila'in ya auku.

Ya zuwa yanzu an an gano gawarwakin mutane 297 da suka hada da kananan yara 109.

Kuma har ya zuwa yanzu ba a gama  tantance adadin mutanen da suka rasu ba, da farko dai ministan lafiya na kasar yace adadin ya kai mutum 500 yayin da dama kuma har yanzu ba'a gano su ba. a gobe Alhamis ne ake sa ran za'a yi jana'izar wadanda suka rasa rayukan nasu.