An Bukaci Karfafa Matakan Tsaro A Sansanonin 'Yan Gudun Hijra A Najeriya
Shugaban hukumar dake kula da 'yan gudun hijra a Najeriya ya bukaci a karfafa matakan tsaro a sansanonin 'yan gudun hijra.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Ernest Mutanga shugaban hukumar dake guda da 'yan gudun hijra a Najeriya cikin wani bayyani da ya fitar a wannan laraba ya bukaci gwamnati da ta kara karfafa matakan tsaron da ya dace domin kare 'yan gudun hijra kimanin miliyan biyu da rikicin boko haram ya raba da mahalinsu.
Gabatar da wannan bukata na zuwa ne bayan harin ta'addancin da aka kai jiya talata a wani kauye dake kewaye birnin maiduguri na jihar borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya, harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30 tare da jikkatar wasu 83 na daban.
Shugaban hukumar dake guda da 'yan gudun hijrar ya ce idan har gwamnati ba ta kara karfafa matakan tsaron da suka dace ba, to mai yiyuwa sansanonin 'yan gudun hijrar su fuskanci hare-haren ta'addanci na kungiyar boko haram.