'Yan Sandar Kasar Kenya Sun Kai Farnmaki Kan Ma'aikatun 'Yan Adawa
(last modified Wed, 16 Aug 2017 19:21:38 GMT )
Aug 16, 2017 19:21 UTC
  • 'Yan Sandar Kasar Kenya Sun Kai Farnmaki Kan Ma'aikatun 'Yan Adawa

Jami'an 'yan sandar kasar Kenya sun kai farmaki kan ma'aikatun fararen hula da masu adawa da sakamakon zaben shugaban kasa na baya bayan nan.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a wannan laraba, jami'an 'yan sandar kasar kenya  tare da ma'aikatan karbar haraji sun kaifarmaki kan ginin ma'aikatar wani mai rajin kare hakin bil-adama, wanda a makun da ya gabata yayi muhara mai zafin gaske game da yadda aka tsara zaben shugaban kasar tare da zarkin gwamnatin Uhuru kenyatta da tamba magudi, saidai ma'aikatar wannan ma'aikata sun ki karbar kiran jami'an tsaro tare da rufe ma'aikatar.

Gwamnatin kenyar dai na zarkin wannan cibiya da wasu cibiyoyin kare hakin bil-adama na daban da laifin rashin biyan haraji, tare da barazanar rufe su.

'Yan adawa da kungiyoyin fararen hula gami da na kare hakin bil-adama na zarkin gwamnatin kasar ta kenya da tabka magudi a zaben shugaban kasar da ya gudana  makun da ya gabata.

Saidai masu sanya ido na cikin gida da na kasashen wajen sun ce an gudanar da zaben cikin 'yanci da adalci, amma shugaban 'yan adawa  Raila Odinga yayi watsi da sakamakon zaben.