RD Congo : Zabtarewar Kasa Ta Yi Ajalin Mutum 40
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23270-rd_congo_zabtarewar_kasa_ta_yi_ajalin_mutum_40
Rahotanni daga Jamhuriya Demukuraddiyar Congo, na cewa mutane arba'in ne suka rasa rayukansu sakamakon zaftarewar kasa da aka samu a wani kauyen masinta a Ituri dake arewa maso gabashin kasa.
(last modified 2018-08-22T07:00:33+00:00 )
Aug 17, 2017 06:15 UTC
  • RD Congo : Zabtarewar Kasa Ta Yi Ajalin Mutum 40

Rahotanni daga Jamhuriya Demukuraddiyar Congo, na cewa mutane arba'in ne suka rasa rayukansu sakamakon zaftarewar kasa da aka samu a wani kauyen masinta a Ituri dake arewa maso gabashin kasa.

Lamarin dai ya biyo bayan ruwan sama da aka tafka tamakar da bakin kwarya a yankin a cewar wata majiya kusa da hukumomin kasar.

Shi ma da yake tabatar da lamarin ga kamfanin dilancin labaren AFP, mukadanshin gwamnan yankin Pacifique Keta, ya ce mutanen 40 sun rasa rayukansu a yayin da wani bangare na tsaunukan ya fado, inda kuma aka samu zaftarewar kasa a yakin na Tora dake kusa da gabar tafkin Albert.