Pira Ministan Congo Brazzaville Ya yi Murabus Daga Kan Mukaminsa.
A jiya alhamis ne Pira ministan kasar ta Jamhuriyar Congo Brazzaville, Clement Mouamba ya yi murabus din tare da ministocinsa.
Murabus din pira ministan ya biyo bayan furucin da shugaban kasar Debnis Sassou N'Guesso ya yi na cewa yana son kafa sabuwar gwamnati wacce za ta fuskanci matsalolin tattalin arzikin kasar.
A ranar talatar da ta gabata ne dai shugaban kasar ya sanar da cewa kasar Congo Brazzaville tana fuskantar matsalolin tattalin arziki. Bugu da kari, shugaba Sassou N'Guesso ya ce; Matsalar ta fara ne daga kan kudi, amma a yanzu ta shafi dukkanin bangarorin tattalin arziki da kasafin kudi da hannun jari.
Sai dai shugaban kasar ya jaddada cewa matsalar da kasar take fuskanta za a iya magance ta.