Shugaban Majalisar Dokokin Burkina Faso Ya Rasu
Aug 19, 2017 11:08 UTC
Allah ya yi wa kakakin majalisar dokokin Burkina faso rasuwa a yau Asabar a birnin Paris na ksar Faransa.
Salifu Diallo ya rasu yana da shekaru 60 a duniya, kamar yadda wata gwamnatin kasar ta sanar a yau ba tare da karin haske ba, saidai wata majiyar diflomatsiya a Braxulls ta ce an iske jami'in ba rai a wani Otel dake birnin na Paris.
A watan Disamba ne shekara 2015 ne aka zabi marigayin a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar, kafin daga bisani a nada shi shugaban jam'iyyar MPP mai mulki a kasar ta Burkina faso.
kafin hakan kuma ya rike mukamai da dama a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Blaise Compaoré.
Tags