Nijeriya : Yau Buhari Zai Koma Gida Daga Landan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23330-nijeriya_yau_buhari_zai_koma_gida_daga_landan
Fadar shugaban kasa a Najeriya ta ce yau Asabar ce, shugaban kasar Muhammadu Buhari zai koma gida daga hutun rashin lafiyar da yake a birnin Landan.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 19, 2017 06:39 UTC
  • Nijeriya : Yau Buhari Zai Koma Gida Daga Landan

Fadar shugaban kasa a Najeriya ta ce yau Asabar ce, shugaban kasar Muhammadu Buhari zai koma gida daga hutun rashin lafiyar da yake a birnin Landan.

Wata sanarwa dake dauke da sa hannun kakakin fadar shugaban kasar Femi Adesina ta ce shugaban zai yiwa 'yan kasar jawabi a ranar Litini mai zuwa.

A ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata ne dai Buhari ya sake komawa Landan domin jinya, inda ya shafe sama da watanni uku, batun da ya janyo kace nace ba kadan ba a kasar ta Najeriya.

Har kawo yanzu dai ba'a sanar da ainahin ciwon dake damun shugaban mai shakaru 74 ba.