'Yan Adawan Kenya Sun Shigar Da Kara Kan Sakamakon Zaben Shugaban Kasa
'Yan adawan kasar Kenya sun shigar da kara kotun koli ta kasar suna masu watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka sanar na cewa shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta shi ne ya lashe zaben.
Rahotanni daga kasar Kenyan sun bayyana cewar a cikin wata sanarwa da hadin gwiwan 'yan adawan kasar Kenyan (NASA) suka fitar sun ce lauyoyin 'yan adawan sun shigar da karar tare da dalilai da suke tabbatar da an aikata ba daidai ba a yayin zaben, don haka suka bukaci da a soke zaben.
Tun da fari dai magudun 'yan adawan wanda kuma ya sha kaye a zaben Raila Odinga yayi watsi da sakamakon zaben da ya ce an tabka magudi, duk kuwa da kore yiyuwar hakan da masu sa ido na kasa da kasa suka yi.
Hukumar zaben kasar Kenyan dai ta sanar da Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 8 ga watan Augustan nan bayan da ya sami kashi 54 cikin dari na kuri'un da aka kada din.