Bukatar 'Yan Adawar Kenya Na Soke Zaben Shugaban Kasa
(last modified Sun, 20 Aug 2017 06:21:57 GMT )
Aug 20, 2017 06:21 UTC
  • Bukatar 'Yan Adawar Kenya Na Soke Zaben Shugaban Kasa

'Yan Adawa a kasar Kenya sun bukaci gwamnati da ta soke zaben shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya na nakalto madugun 'yan adawa na kasar Kenya Raila Odinga a jiya assabar na cewa zaben da aka gudanar na shugaban kasar ranar takwas ga watan Augustan  an tabka magudi, kuma ba zai  iya amincewa da sakamakon zaben ba shi da magoya bayansa ba.

Hukumar zaben kasar Kenya dai ta bayyana cewa Uhuru Kenyatta ya samu nasarar lashe zaben da ya gudana a ranar takwas ga watan Agustan da muke ciki, da kuri’u miliyan daya da dubu dari hudu, sakamakon da Odinga yayi watsi da shi, bisa ikirarin an tafka magudi cikinsa.

A halin yanzu dai matakin Raila Odinga na komawa ga kotu, maimakon jagorantar zanga-zanga, ya sanya hankulan ‘yan kasar ta Kenya sun kwanta, idan akai la’akari da yadda akalla mutane 1,200 suka rasa rayukansu biyo bayan rikicin da ya barke bayan zaben shugabancin kasar da aka yi a shekarar 2007.