Ranar Haihuwar Mugabe Ta Zama Ranar Hutu A Zimbabwe
Aug 20, 2017 11:15 UTC
Ranar 21 ga watan Fabrairu wacce ta yi daidai da ranar haihuwar shugaba Robert Mugabe, zata kasance hutu a ko wacce zagayowarta a wannan kasa.
Jaridar Herald mallakin gwamnatin kasar ta Zimbabwe ta rawaito labarin cewa za'a dinga hutu a ko wacce zagayowar ranar haihuwar shugaban kasar
Robart Mugabe dan shekaru 93 na shugabancin wannan kasar ta Zimbabwe ne tun cikin 1980.
Lamarin ya bayyana ware kebe wannan ranar a matsayin nuna karamci ne ga shugaban kasar kamar yadda jaridar ta rawaito ministan cikin gidan na kasar na fada.
Duk da yawan shekarunsa Mugabe ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar mai zuwa na 2018.
Tags