Burkina Faso: An yi Zanga-zangar Yin Tir Da Ayyukan Ta'addanci.
(last modified Sun, 20 Aug 2017 18:15:48 GMT )
Aug 20, 2017 18:15 UTC
  • Burkina Faso: An yi Zanga-zangar Yin Tir Da Ayyukan Ta'addanci.

Daruruwan mutanen kasar ne su ka shiga cikin Zana-zangar da aka yi a birnin Ouagadougou, domin yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai wa kasar.

Tashar telbijin din France 24 ta ce; Masu Zanga-zangar da su ka yi ta cikin shiru ba tare da yin mgana ba, sun ba ta sunan; sakon hadin kai domin kalubalantar ayyukan dabbanci.

Har ila yau, masu Zanga-zangar sun bayyana cewa shirun da suka yi yana nufin cewa basu tsoron 'yan ta'adda, kuma za su yi tsayin daka domin kalubalantarsu.

A ranar 13 ga watan Augusta ne dai aka kai hari a babban birnin kasar Ouagadougou, wanda ya ci rayukan mutane 19 da jikkata wasu da dama.