Kasashen Masar Da Somaliya Sun Jaddada Bukatar Bunkasa Alaka A Tsakaninsu
Shugabannin kasashen Masar da Somaliya sun jaddada bukatar bunkasa alakar kasuwanci da na tattalin arziki a tsakanin kasashensu.
A ziyarar aikin da shugaban kasar Somaliya Muhammad Abdullahi Muhammad ya kai zuwa birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Lahadi ya gana da shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi, inda shugabannin biyu suka jaddada bukatar gudanar da taimakekkeniya a tsakaninsu a bangarori da dama musamman bunkasa harkar kasuwanci da na tattalin arziki.
Shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi ya gabatar da shawara ga kasar Somaliya kan bude cibiyoyin kasuwancinta a kasar Masar da nufin bunkasa harkar tattalin arzikin kasar.
A nashi bangaren shugaban kasar Somaliya Muhammad Abdullahi Muhammad ya jaddada bukatar habaka harkar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Kamar yadda shugabannin biyu suka tattauna batun ayyukan ta'addanci da kasashensu suke fuskanta musamman yadda mayakan kungiyar Al-Shabab suke kai jerin hare-haren wuce gona da iri a sassa daban daban na kasar Somaliya, inda ita ma Masar take fama da ayyukan ta'addanci a lardin Sina ta Arewa.