MDD: Akwai Bukatar Isar Da Taimako Ga Wasu Al'ummomin Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23412-mdd_akwai_bukatar_isar_da_taimako_ga_wasu_al'ummomin_sudan
Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, akwai bukatar kasashen duniya masu taimakawa da su bayar da gudunmawa domin taimaka ma wasu al'ummomi a kasar Sudan.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 21, 2017 14:45 UTC
  • MDD: Akwai Bukatar Isar Da Taimako Ga Wasu Al'ummomin Sudan

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, akwai bukatar kasashen duniya masu taimakawa da su bayar da gudunmawa domin taimaka ma wasu al'ummomi a kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a lokacin dayake zantawa da manema labarai yau a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan, babban jami'in majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan jin kai Marta Ruidas ya bayyana cewa, abin da aka samu domin taimaka masu matsala a Sudan bai wuce kashi 23 cikin dari ba.

Ya ce a halin yanzu akwai mutane kimanin miliyan 2 da dubu 500 da suke da butar taimako ba tare da bata lokaci ba, kuma kudaden da suke hannu a yanzu ba za su isa gudanar da wannan aiki ba.

Ya ce kudaden da suka samu daga farkokn wanann shekara ya zuwa domin gudanar da aikin jin kai a Sudan, ba su dala miliyan 570 ba.