An Halaka Wani Kwamandan 'Yan Ta'addan Al-shabab A Kasar Somalia
Jami'an sojin kasar Somalia sun sanar da samun nasarar halaka 7 daga cikin mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shabab.
Kamfanin dillancin labaran Al Afrika ya bayar da rahoton cewa, rundunar sojin ta Somalia ta sanar a yau cewa, dakarunta sun kaddamar da wannan farmaki ne a garin Jillit da ke kudancin birnin Magdishou fadar mulkin kasar, inda suka halaka wani babban kwandan kungiyar mai suna Ali Muhammad Hussain, da ake yi wa lakabi da Ali jibal, tare da masu gadinsa su shida.
Bayanin ya ce an gudanar da wannan farnaki ne tare da amincewar shugaban kasar ta Somalia Muhammad abdullah Muhammad.
Kungiyar Al shabab dai reshe ne na kungiyar 'yan ta'adda ta Alqaida a Somalia, kuma tana kaddamar da hare-haren ta'addanci a cikin kasar da kuam ksashen da ke makwabtaka da ita.