WHO Ta Yi Gargadin Yaduwar Cututtuka A Saliyo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23432-who_ta_yi_gargadin_yaduwar_cututtuka_a_saliyo
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi gargadin cewa, akwai yiwuwar yaduwar wasu cututtuka kamar amai da gudawa da zazzabin sauro a Saliyo, bayan iftiila'in ambaliyar ruwa da zaftarewar laka da ta auku a makon da ya gabata a kasar, wacce ta hadassa mutuwar mutane 500.
(last modified 2018-08-22T07:00:35+00:00 )
Aug 22, 2017 06:27 UTC
  • WHO Ta Yi Gargadin Yaduwar Cututtuka A Saliyo

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi gargadin cewa, akwai yiwuwar yaduwar wasu cututtuka kamar amai da gudawa da zazzabin sauro a Saliyo, bayan iftiila'in ambaliyar ruwa da zaftarewar laka da ta auku a makon da ya gabata a kasar, wacce ta hadassa mutuwar mutane 500.

WHO ta kara da cewa, bisa la'akari da lalacewar hanyoyin ruwa da kayayyakin tsaftace muhalli, mazauna yankunan da iftila'in ya shafa a kasar dake yammacin Afrika na cikin hadarin fuskantar barkewar cututtukan.

 Ko a shekarar 2012 ma dai an samu barkewar cuwar kwalara a kasar ta Saliyo.

A yanzu haka, WHO ta ce tana aiki da hukumomin lafiya na kasar ta Saliyo domin kara kaimi wajen daukar matakan kariya da kuma tunkarar barkewar cututtuka.