Yau Ne Za'a Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Angola
A yau ne ake sa ran al’ummar kasar Angola za su kada kuri’ar zaben 'yan majalisar kasar da zai share fagen zaben sabon shugaban kasar wanda zai maye gurbin shugaba Jose Eduardo Dos Santos wanda ya shafe kimanin shekaru 38 yana mulkin kasar.
Rahotanni daga kasar Angolan sun bayyana cewar kimanin mutane miliyan 9 ne suka cancanci kada kuri'ar ta su a zaben na yau da za a fafata tsakanin 'yan takaran jam'iyyu shida na kasar da suka hada da Jam'iyyar MPLA mai mulki da babbar jam'iyyar 'yan adawa ta UNITA, sai kuma jam'iyyar CASA-CE (wacce ta balle daga jam'iyyar UNITAn), sai kuma jam'iyyun FNLA, PRS da kuma APN.
A bisa kundin tsarin mulkin kasar Angolan na shekara ta 2010 duk jam'iyyar da ta fi samun kujeru a majalisar kasar mai kujeru 200, to shugaban jam'iyyar ne zai zama shugaban kasa. A saboda haka ne ake ganin da wuya idan ba dan takarar jam'iyyar MPLA mai mulki kuma ministan tsaron kasar Joao Lourenco ne zai zama sabon shugaban kasar ba bisa la'akari da irin tasirin da jam'iyyar take da shi a matsayin wacce take mulkin kasar tun bayan samun 'yancin kanta.
A watan Disambar bara ce dai shugaba Jose Eduardo dos Santos, dan shekaru 74 a duniya ya sanar da cewa ba zai sake neman wani wa'adin mulki na kasar ba, inda jam'iyyarsa ta MPLA din ta sanar da Mr. Joao Lourenco a matsayin dan takararta wanda kuma ake sa ran zai gaji Mr. dos Santos din.