Mahukunta A Kasar Masar Sun Kame Masu Fataucin Sassan Jikin Bil-Adama
(last modified Wed, 23 Aug 2017 19:01:11 GMT )
Aug 23, 2017 19:01 UTC
  • Mahukunta A Kasar Masar Sun Kame Masu Fataucin Sassan Jikin Bil-Adama

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kame wasu gungun mutane 12 ciki har da likitoci da ma'aikatan jiyya da suke fataucin sassan jikin bil-Adama.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ta watsa rahoton cewa: Jami'an tsaron  kasar sun yi nasarar kame likitoci uku da jami'an jiyya hudu da ma'aikatan asibi uku gami da wasu dillalai biyu da suke nemo mutanen da suke son sayar da wasu sassan jikinsu a kan wasu kudade da aka cimma yarjejeniya a kai.

Rahoton ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ya kara da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kame gungun mutanen ne a daidai lokacin da suke gudanar da aikin fida domin cire koda da hanatar mutanen da suka sayar da nasu da nufin samun kudaden bukatu a wani asibiti mai zaman kansa.

Tuni dama Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana kasar Masar daga cikin jerin kasashen da suka yi kaurin suna a fagen sayar da sassan jikinsu domin yin fataucinsu zuwa wasu kasashe da nufin dasawa masu bukatarsu.