AU Ta Jajantawa Kasashe Mambobinta Sanadin Rasa Rayuka A Ambaliyar Ruwa
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta jajantawa kasashe mambobinta bisa rasa rayuka sanadiyyar ambaliyar ruwa da zaftarewar laka da aka samu wacce ta yi ajalin daririwan mutane.
Wakiliyar shugaban kungiyar ta AU ta isa kasar Saliyo domin duba irin barnar da zaftarewar laka ta haddasa a ranar 15 ga watan Augasta a kasar, kana da mika kayayyakin tallafi.
Sanarwar da AU ta fitar tace, shugabar sashen walwalar jama'a ta kungiyar Amira Elfadil, ta isa birnin Freetown ne tun a ranar Talata, domin bayyana goyon bayan AU da kuma tallafawa gwamnatin Saliyo sakamakon ibtila'in da ya afku.
AU zata mika cakin kudi na dalar Amurka dubu 100 a matsayin wani bangare na gudumowar da AU ta baiwa gwamnatin Saliyo, sakamakon ibtila'in zaftarewar laka, wanda yayi sanadiyyar hallaka akalla mutane 500, kana wasu sama da 600 suka bace, sannan wasu dubban mutane suka rasa matsugunansu.
Bugu da kari, a wata sanarwar ta daban, shugaban na AU ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnatin Guinea da ta jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC, sakamakon bala'in da aka samu a kasashen wanda ruwan sama ya haddasa.