Wani Jirgin Saman Yaki A Tarayyar Nigeria Ya Fadi A Jihar Kaduna
Wani Jirgin saman yaki mallakin rundunar sojojin sama na Nigeria, samfurin "Air Beetle" ya fadi a jiya Alhamis kuma kashe matukin jirgin a birnin Kaduna
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto Air Commodore Olato-kunbo Adesanya kakakin rundunar sojojin sama na kasar yana fadar haka, ya kuma kara da cewa matukin jirgin wanda kuma shi kadai a cikin sa, abin bakin ciki" ya rasa ransa a hatsarin.
Air Commondore Adesanya ya ce har yanzun ba'a san musabbabin faduwar jirgin ba, amma tuni babban komandan sojojin sama na kasar ya kafa komiti na musamman don bincike da kuma gano musabbabin hatsarin na kusa da nesa. Ya kuma bayyana hatsarin a matsayin tunatarwa ga irin hatsarin da ke tattare da tukin jiragen sama.
Adesanya ya kammala da cewa babban komandan sojojin saman na kasar da kuma rundunar sojojin sama sun jajantawa iyalai da kuma dangin matukin jirgen da ya rasa ransa.