Shugaba Buhari Ya Gana Da Jami'an Jam'iyyun APC Da PDP Na Najeriya
(last modified Fri, 25 Aug 2017 16:37:27 GMT )
Aug 25, 2017 16:37 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Gana Da Jami'an Jam'iyyun APC Da PDP Na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayi wata ganawa da shugabannin babbar jam'iyyar adawa ta kasar PDP da kuma jam'iyyarsa ta APC mai mulki a fadar gwamnati da ke birnin Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewar da misalin karfe 11:10 na safiyar yau Juma'a ne shugaba Buharin ya gana da manyan jami'an jam'iyyar ta PDP karkashin jagorancin shugabanta Ahmed Makarfi da kuma tawagar shugabannin APC din karkashin jagorancin shugabanta na kasa John Odigie-Oyegun a lokacin da suka kai masa ziyarar maraba da dawowa da kuma tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi kasar.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriyan NAN ya ce a yayin ganawar an tattauna batutuwan da suka shafi zamantakewa da kuma yanayin siyasa a kasar musamman batun kalaman batanci da wasu 'yan siyasa da masu sharhi suke yi bugu da kari kan batun yanayin matsalar tsaro da ake fuskanta.

Wasu majiyoyin sun bayyana cewar a yayin  ganawar wacce aka yi ta ba tare da an bar 'yan jarida sun shiga ba, shugaba Buhari ya gode wa jagororin jam'iyyun biyu saboda ziyarar da suka kawo masa da kuma kiransu da su isar da sakon godiyarsa ga al'ummominsu saboda irin addu'oin samun sauki da suka dinga yi masa, yana mai cewa taron na yau na nuni da irin hadin kan da ake da shi a kasar.

Shi ma a nasa bangaren shugaban jam'iyyar PDP din Ahmad Makarfi ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta PDP a shirye take ta ba da hadin kai ga gwamnatin wajen ci gaban kasa.