An yi barazanar kai hari kan jami'an kasar Burkina Faso
(last modified Sun, 13 Mar 2016 09:47:41 GMT )
Mar 13, 2016 09:47 UTC
  • An yi barazanar kai hari kan jami'an kasar Burkina Faso

Wata Kungiya dake dauke da makamai a kasar Burkina Faso ta yi barazanar kaiwa Jami'an tsaron kasar hai matukar ba a saki mutananta ba.

A wata sanarwa da ta fitar jiyar Assabar Kungiyar Koglweogo ta yi barazanar kai hari kan gidan kaso na garin Fada N'Gourma dake gabashin kasar domin kubuto mutanan ta goma dake tsare a gidan kaso.

Majiyar tsaron kasar ta tabbatar da cewa yanzu haka 'yan kungiyar da adadinsu ya haura zuwa dubu daya da 500 na tururuwa zawa garin Fada N'Gourma daga arewa da kuma kudancin kasar

Majiyar ta kara da cewa 'yan kungiyar ta Koglweogo na iya kaddamar da komai domin 'yanto magoya bayansu dake gidan yarin.

A daren juma'ar da ta gabata hukumar Jandarma ta sanar da cewa take taken 'yan kungiyar Koglweogo na nuni da cewa suna janyo ra'ayin makoya bayansu da su tattaru a garin Fada N'Gourma domin kai farmaki a gidan kason birnin su kuma kubutar da 'yan uwansu dake ciki.