Al-Shabab Ta Tabbatar Da Halaka Daya Daga Cikin Manyan Kwamandojinta
(last modified Sun, 27 Aug 2017 04:56:34 GMT )
Aug 27, 2017 04:56 UTC
  • Al-Shabab Ta Tabbatar Da Halaka Daya Daga Cikin Manyan Kwamandojinta

Kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab ta kasar Somaliya ta tabbatar da halaka daya daga cikin manyan kwamandojinta sakamakon harin da sojojin kasar da kawayensu na waje suka kai masa.

Kungiyar al-Shabab din wacce ta ke da alaka da kungiyar ta'addancin nan ta Al-Qa'ida ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta watsa a jiya Asabar ta hanyar yanar gizo inda ta ce an hallaka Ali Mohammed Hussein wanda aka fi sani da Ali Jabal ne sakamakon harin da aka kai masa ta sama.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin kasar Somaliyan suka sanar da cewa dakarun sojin kasar da kawayensu na kasashen waje sun hallaka Ali Jabal din da aka ce yana da hannu cikin hare-haren ta'addancin da 'yan kungiyar Al-Shabab din suke kai kasar Somaliyan.

A lokuta da dama dai kungiyar al-Shabab din dai suna kai munanan hare-hare birnin Mogadishu, babban birnin kasar Somaliyan da nufin kifar da gwamnatin kasar wacce ta ke cikin mummunan yanayin rashin tsaron tun bayan da aka kifar da gwamnatin Siad Barre na kasar a shekara 1991.