Madugun 'Yan Adawan Angola Ya Nuna Rashin Amincewa Sakamakon Zaben Kasar
(last modified Sun, 27 Aug 2017 04:57:21 GMT )
Aug 27, 2017 04:57 UTC
  • Madugun 'Yan Adawan Angola Ya Nuna Rashin Amincewa Sakamakon Zaben Kasar

Magudun babbar jam'iyyar adawar kasar Angola (UNITA) ya bukaci hukumar zaben kasar da ta yi bayanin yadda aka yi ta sanar da cewa jam'iyyar MPLA mai mulki ne ta lashe zaben 'yan majalisar kasar da aka gudanar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo Isaias Samakuva, magudun jam'iyyar UNITAn yana fadin cewa daga ina aka sami wannan sakamakon zaben da aka sanar, a saboda haka ya zama wajibi hukumar zabe ta CNE ta yi wa al'ummar Angola bayanin me ya faru ne sannan daga ina aka samo wadannan kuri'un.

Mr. Samakuva ya kara da cewa jam'iyyar ta su ta UNITA tana ci gaba da kidayen kuri'un daga runfunan zabe da kuma na'urorin kwamfuta wadanda sun yi hannun riga da sakamakon da hukumar zaben ta sanar.

Hukumar zaben kasar Angolan dai ta sanar da cewa jam'iyyar MPLA mai mulki ita ce ta lashe zaben da aka gudanar da sama da kashi 61 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben da masu sanya ido na kasa da kasa suka ce an gudanar da shi cikin adalci.

Bayan sanar da sakamakon zaben na gaba daya dai ana sa ran Joao Lourenco, tsohon ministan tsaron kasar shi ne zai zama shugaban kasa da zai maye gurbin shugaba Jose Eduardo dos Santos, wanda ya mulki kasar har na tsawon shekaru 38.