Nijar Ta Musunta Karbar Kudade Don Mika Dan Gaddafi Ga Libiya
Gwamnatin Nijar ta musunta cewa ta karbi kudade domin mika dan tsohon shugaban kasar Libiya, Sa'adi Ghaddafi ga mahukuntan Libiya.
A watan Satumba na shekara 2011 ne Sa'adi Gaddafi ya yi gudun hijira a Jamhuriya Nijar, gabanin hambararda gwamnatin mahaifinsa.
A 'yan kwanakin nan dai wasu kafofin yada labarai a Libiya na rawaito wata wasika da Sa'adi Gaddafi ya aike ga mai shigar da kara na Libiya, inda ya zargi firaministan lokacin Ali Zeidan da zubawa gwamnatin Nijar kudade Dala Miliyan hudu domin tiso keyar shi.
A watan Maris 2014 ne gwamnatin Nijar ta mikawa gwamnatin Libiya Sa'adi Gaddafi, saidai a wata wasika daga bangaren yada labari na fadar firaministanta kasar ta Nijar, nisanta kanta ta yi da wannan batu, tana mai cewa ba shi da tushe balle makama.
Gwamnatin ta NIjar ta ce ita kawai abunda ta sani shi ne cewa ta samu tabbaci daga gwamnatin ta Libiya cewa zatayiwa Sa'adin Gaddafin adalci da kuma kula ta gari idan ya koma kasarsa, tare da cewa ta ji takaici kan yadda hakan bata samu ba ga dan tsohon shugaban Libiya data bawa mafakar jin kai.
kafin hakan dai Nijar ta jima tana fadar cewa Sa'adin Ghasdafin babbar barazana ce a cikin kasarta, kasancewar yana firta wasu kalamai dakan iya tada fitina tun daga cikin kasarta.