Najeriya : Evans Ya Amsa Laifinsa Bisa Barazana _ Lauyansa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23679-najeriya_evans_ya_amsa_laifinsa_bisa_barazana_lauyansa
Shahararen mai garkuwa da mutane a Najeriya mai suna Evans, ya amsa laifin da ake tuhumarsa na garkuwa da mutane a gaban kotun Legas.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 30, 2017 10:50 UTC
  • Najeriya : Evans Ya Amsa Laifinsa Bisa Barazana _ Lauyansa

Shahararen mai garkuwa da mutane a Najeriya mai suna Evans, ya amsa laifin da ake tuhumarsa na garkuwa da mutane a gaban kotun Legas.

Saidai lauyen dake karesa, Olukoya Ogungbeje, ya ce Evans din ya amsa laifin ne bisa ga barazanar 'yan sanda.

A cikin wata wasika da ya aikewa kamfanin dilancin labaren AFP, Ogungbeje ya ce Evans ya bayyana masa karara cewa 'yan sanda sun umurce shi da ya amsa laifin ko kuma su kashe shi.

Sannan lauyen na sa ya ce baida ma labarin Evans zai gurfana gaban kotu yau Laraba, ya dai ji labarin ne ta hanyar kafofin sadarwa na zamani da yammacin jiya, wanda sabilin hakan bai ma samu lokacin kimsawa ba don halartar zamen kotun.

Laiyan ya ce Evans zai canza maganarsa zuwa kin amuncewa da laifin a zamen kotun na ranar 19 ga watan Oktoba mai zuwa.

A ranar 10 ga watan Yuni da ya gabata ne aka cafke Evans wanda akewa lakabi da sarkin garkuwa da mutane a Najeriya.