Hare Haren Mayakan Kungiyar Yan Ta'adda Ta Somalia A Kasar Kenya
(last modified Thu, 31 Aug 2017 06:25:16 GMT )
Aug 31, 2017 06:25 UTC
  • Hare Haren Mayakan Kungiyar Yan Ta'adda Ta Somalia A Kasar Kenya

Hare-Haren yan ta'adda a daren ranar Talatan da ta gabata ya yi sanadiyyar raunata mutum gusa, sannan yan ta'addan sun arce zuwa kan iyakokin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin Labarai na Xinhuwa na kasar China ya nalati majiyar jami'an tsaro na kasar Kenya ta kara da cewa mayakan na Al-shabab sun tare zawa kan iyakokin kasar bayin harin. 

Majiyar ta kara da cewa hare haren sun auku ne a yankunan Dabacity da kuma Mandera dake arewa maso gabacin kasar. majiyar ta kara da cewa kafin wannan haein mayakan kungiyar ta al-shababn sun sun lalata wasu hanyoyin sadarwa ta wayar tarho a yankunan kafin su gudu zuwa cikin kasar Somalia. 

Kafin haka dai kwanaki ukku da suka gabata  mayakan na Al-shabab sun kai wani hari da bom a cikin lardin Mandera inda suka kashe jami'an tsaron kasar guda biyu . 

Hare-haren mayakan al-shabban kan kasar Kenya ya jawo mutuwar jami'an da dama, mafi yawansu jami'an tsaron kasar.