Likitoci A Asbitocin Gwamnatin Sun Bada Sanarwan Shiga Yajin Aiki A Nigeria
Kungiyar likitoci masu koyon karatu sun bada sanarwan fara yajin aiki na gama gari a duk fadin kasar don neman wasu hakkokinsu wadanda suka makali a hannun gwamnatocin tarayyar da kuma na jihohi a ranar 4 ga watan satumba mai kamawa.
Jaridar Primium times ta Nigeria ta nakalto shugaban kungiyar likitocin wacce aka fi sani da NARDs a takaice Dr Olushegun Olaopa na jami'ar koyon aikin likita ta Ibadan yana bada wannan sanarwan a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa a ranar Litinin dukkan yayan kungiyar zasu dakatar da aiki don takurawa gwamnatoci kan albashinsu da kuma wasu bukatunsu da suka makale a wajensu.
Olushegunn ya ce a ranar 26 ga watan Augustan da muke ciki ne shuwagabannin kungiyar suka gudanar da tare a Abuja don tattauna matsalolin kungiyar da kuma matakan da zasu dauka don warwaresu. shi ne a karshen taron suka tsaida ranar 4 ga watan Satumba don fara yajin aiki na sai baba ta gani, sai har an bayasu hakkokinsu.
Shugaban kungiyar ta NARDs ya kammala da cewa zasu gudanar da yajin aikin gargadi a ranar 30 ga watan Augusta a dukkan rassansu dake dukkan jihohin kasar .